Skip to main content

Posts

Showing posts from October, 2022

Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta naɗa Kwamishinan ma'aikatan ilimin matakin farko da Kwamishinan mata a matsayin masu bawa kungiyar shawara

 Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta naɗa Kwamishinan ma'aikatan ilimin matakin farko da Kwamishinan mata a matsayin masu bawa kungiyar shawara.  A Ranar Laraba, kungiyar BUNI-GUBANA WOMEN & YOUTH NETWORK karkashin jagorancin Hajiya Fatima Gwamnaty Mairiga ta ziyarci ofishin Kwamishinan ma'aikatan ilimin matakin farko Dr. Muhammad Sani Idriss da Kwamishinan ma'aikatan mata Hajiya Hauwa Abubakar a matsayin masu bawa kungiyar shawara.  Kwamishinonin sun yaba da ƙokarin matasa da matan da suka ƙirkiro Kungiyar don ƙokarin "rama alkhairi da alkhairi' . Ma'ana, bada zunzurutun gudumawa da hidima tuƙuru ga Gwamnatin Mai Mala Buni da Hon. Idi Barde Gubana don ta cigaba da inganta rayuwar Jahar Yobe. Hajiya Mairiga ta samu rakiyar wasu daga cikin shugabannin kungiyar.

Kungiyar Buni Gubana Women & Youth network ta fara shiriye-shiriyen gudanar da manya-manyan tararruka a Yobe zone-A , zone-B da zone-C.

 Kungiyar Buni Gubana Women & Youth network ta fara shiriye-shiriyen gudanar da manya-manyan tararruka a Yobe zone-A , zone-B da zone-C.  A yau Talata, kungiyar Buni Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Gwamnaty Mairiga ta fara shiriye-shiriyen gudanar da manya-manyan tararruka na ƙaddamar da shugabanninta na Yobe shi'ar gabas, shi'ar kudu da shi'ar arewa.  Kamar yadda a baya Kungiyar ta ƙaddamar da shugabanninta na jaha, yanzu haka ta fara shiriye-shiriyen ƙaddamar da na shi'oin uku na jahar, daga nan kuma sai na ƙananan hukumomi 17 da gundumomi 178 na Jahar Yobe baki daya.  Kungiyar, wanda matasa da mata na Jahar Yobe suka hadu suka ƙirkiro da ita don su bada gudumawarsu wa Gwamnatin Mai Mala Buni don ta cigaba da kyawawan manufofin cigaban Jahar Yobe da ta ɗauko kuma mutane suke moran ta a zahiri. Kama daga; ayyukan cigaban matasa da dama, bawa matasa dama a Gwamnatinsa, inganta rayuwar mata-da-yara musamman wajen kiwon lafiya,...

Kungiyar Buni - Gubana Women & Youth Network ta kai ziyara na musamman ofishin Tijjani Musa Tumsa a Abuja.

 Kungiyar Buni - Gubana Women & Youth Network ta kai ziyara na musamman ofishin Tijjani Musa Tumsa a Abuja.  ......Kungiyar ta naɗa shi a matsayin memba na komitin amintattu.  Kungiyar Buni - Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Gwamnaty Mairiga ta kai ziyara na musamman ofishin jigo cikin ƴan siyasan Najeria kuma gogeggen Dan siyasan Jahar Yobe Alh. Tijjani Musa Tumsa (TMT) a Abuja.  A cikin jawabanta, Hajiya Fatima ta bayyana cewa "Kungiyar, wanda matasa da mata na Jahar Yobe suka assasata don su bada gudumawarsu wa gwamnatin Mai Mala Buni musamman akan kyawawan manufofin cigaban Jahar Yobe da Gwamnatin da ta ɗauko kuma mutane suke moran ta a zahiri" Mairiga ta ce Insha Allah matasan Jahar Yobe zasu 'rama alkhairi da alkhairi' , saboda ɗaruruwan ayyukan cigaban matasa, bawa matasa muƙaman Gwamnati, inganta rayuwar mata-da-yara musamman wajen kiwon lafiya, bada jari keuta da sauran tsare-tsare masu yawa don inganta rayuwar m...

Kungiyar BUNI-GUBANA WOMEN AND YOUTH NETWORK tana taya mai girma seneta Ahmad Ibrahim lawan murnan samun karramawa na 'GCON' daga shugaban ƙasa Buhari.

 Kungiyar BUNI-GUBANA WOMEN AND YOUTH NETWORK tana taya mai girma seneta Ahmad Ibrahim lawan murnan samun karramawa na 'GCON' daga shugaban ƙasa Buhari. Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Mairiga tana taya mai girma dan majalisar dattija Senata Ahmad Ibrahim lawan murnan samun karramawa na 'GCON' daga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a wajen taron karrama ƴan ƙasa da a ake gudanar da ita a babban dakin taro na International Conference Centre, Abuja.  Bikin an shiriya tane don karrama ƴan Nigeria da suke yin ƙokari wajen bada gudumawarsu don tabbatar da zaman lafiya, hadin kan ƴan ƙasa, yiwa ƙasa hidima da cigaban Najeria baki ɗaya.  Shugaban kungiyar, Hajiya Mairiga tace "mai girma seneta Ahmad Ibrahim lawan ya cancanci wannan karramawan a wajen shugaban ƙasa Muhammadu Buhari duba ga irin gudumawar da yake bayarwa ta fuskan siyasa, zaman lafiya, hadin kan ƴan ƙasa da kawo ɗaruruwan ayyukan cigaban a kasa Najeriya ...

Kungiyar Buni-Gubana Women and Youth Network ta naɗa Kwamishinan jinkai da kula da lamuran agaji, Dr. Abubukar Garba Iliya a matsayin memba na komitin amintattu.

 Kungiyar Buni-Gubana Women and Youth Network ta naɗa Kwamishinan jinkai da kula da lamuran agaji, Dr. Abubukar Garba Iliya a matsayin memba na komitin amintattu. A yau litinin, kungiyar BUNI-GUBANA WOMEN & YOUTH NETWORK karkashin jagorancin Hajiya Fatima Gwamnaty Mairiga ta ziyarci ofishin Kwamishinan jinkai da kula da lamuran agaji na Jahar Yobe, Dr. Garba Iliya a inda ta naɗa shi a matsayin memba na komitin amintattu na kungiyar.  Kungiyar, wanda matasa da mata na Jahar Yobe suka hadu suka ƙirkiro da ita don su bada gudumawarsu wa Gwamnatin Mai Mala Buni don ta cigaba da kyawawan manufofin cigaban Jahar Yobe da ta ɗauko kuma mutane suke moran ta a zahiri.   Kama daga; ayyukan cigaban matasa da dama, bawa matasa dama a Gwamnatinsa, inganta rayuwar mata-da-yara musamman wajen kiwon lafiya, bada jari da sauran tsare-tsare masu yawa wa mata masu juna, jarirai da yara ƙanana.  Buni-Gubana Women & Youth Network ta fito da taken ta "rama alkhairi da alkhair...

Ɗan Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ya zama SSA na Gwamna Mai Mala Buni.

 Ɗan Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ya zama SSA na Gwamna Mai Mala Buni.  Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Gwamnaty Mairiga tana taya Ibrahim Baba Saleh wanda shine Director Media and Publicity na kungiyar zama babban hadimin Gwamna Mai Mala Buni ( Senior Special Assistant, SSA).  Kungiyar tana yiwa mai girma Gwamna Mai Mala Buni tare da mataimakinsa H.E Idi Barde Gubana godiya ba adadi.  Haka zalika, membobin kungiyar suna yiwa Hajiya Fatima Mairiga godiya da jinjina na musamman saboda tsayawa, jajircewa, ƙokari da takeyi don ganin ta saka duk membobin kungiyar farin ciki.  Daga karshe, Hajiya Fatima Mairiga ta jaddawa mai girma Gwamna Mai Mala Buni tare da mataimakinsa H.E Idi Barde Gubana da Jam'iyyar APC baki daya goyon bayanta ɗari bisa ɗari.  Singed Hajiya Fatima Mairiga, State Coordinator na Buni-Gubana Women & Youth Network.  Congratulations Ibrahim Baba Saleh

Gov. Buni Charge Women and Youth on Patriotism

 Gov. Buni Charge Women and Youth on Patriotism The Buni/Gubana Women and Youth Network, today paid a courtesy call on His Excellency, the Executive Governor of Yobe state, Hon. Mai Mala Buni, at Government House Damaturu. Coordinator of the Network, Hajiya Mairiga Umar, described Governor Buni as the most youth and women friendly governor in Nigeria. She said the essence of creating the network was to appreciate the gesture of the governor to women and youth in the state through dedication and selfless service. Mairiga assured that the Network would work for the success of the Governor Buni administration. Governor Buni urged members of the Network to always have the interest of the state at heart. "You are the leaders of tomorrow, you should develop the spirit of patriotism and selfless to the state and country. Gov. Buni commended the Network for the show of love and concern to his government and state. Signed Mamman Mohammed, DG, Press and Media Affairs.

Ƙungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta ziyarci shugaban majalisan Dattawan Nigeria (Senate President) Da mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa a Abuja..

 Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta ziyarci shugaban majalisan Dattawan Nigeria (Senate President) Da mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa a Abuja.. Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Gwamnaty Mairiga ta kai ziyara na musamman ofis ɗin shugaban majalisan dattawan Najeria, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan GCON, da mataimakin shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa (Na Arewacin Najeria), Sanata Abubakar Kyari a Abuja.  Ziyarar, wanda shugaban kungiyar ta jagoranta an fara ta ne da taya shugaban majalisan dattawan murman samun lambar yabo na 'GCON' daga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Haka zalika, kungiyar ta ziyarci Sanata Abubakar Kyari ne don tattaunawa da shi akan lamuran Jam'iyyar APC (a mataki na ƙasa) musamman abubuwan da suka shafi Jam'iyyar da zaɓen 2023. Daga ƙarshe, Ƙungiyar ta yiwa Sanata Ahmed Ibrahim Lawan addu'ar Allahu ya taimake shi, ya dafa masa, sannan ya albarkaci sabuwar lambar yab...

Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta kai tallafi garin Koromari, yankin Dapchi.

 Ambaliyan ruwa: Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta kai tallafi garin Koromari, yankin Dapchi.  Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Gwamnaty Mairiga ta bada gudumawar kayan abinci da kayan amfani-a-gida wa mutanen da iftila'in ruwa yayi musu ta'adi a garin Koromari dake yankin Dapchi, karamar hukumar Bursari.  Tawagar kungiyar, wanda sukayi tafiya na wasu lokuta akan kwale-kwale a cikin ruwa don ƙokarin kai agaji wa bayin Allah wanda iftila'in ambaliyan ya shafe su.  A lokacin ziyarar, Hajiya Mairiga tace "mu kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network munzo ne domin mu jajanta muku akan asarar dukiyoyin ku da kukayi sanadiyar ambaliyan. Shi yasa muka zo muku da wannan tallafin dai-dai karfin mu domin ta rage muku raɗaɗin ɓarnar da ambaliyan yayi muku". Shi kuma a cikin jawabansa, Mai garin, a madadin mutanen garinsa, Koromari, ya fara da jinjinawa kungiyar a kan namijin ƙokari da tayi, "wa...

Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network tana taya Gwamna Mai Mala Buni murnan samun karramawa na 'CON' daga shugaban ƙasa Buhari.

 Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network tana taya Gwamna Mai Mala Buni murnan samun karramawa na 'CON' daga shugaban ƙasa Buhari. Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Mairiga tana taya mai girma Gwamna Mai Mala Buni murnan samun karramawa na 'CON' daga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a wajen taron karrama ƴan ƙasa da a ake gudanar da ita a babban dakin taro na International Conference Centre, Abuja.  Bikin an shiriya tana don karrama ƴan Nigeria da suke yin ƙokari wajen bada gudumawarsu don tabbatar da zaman lafiya, hadin kan ƴan ƙasa, yiwa ƙasa hidima da cigaban Najeria baki ɗaya.  Shugaban kungiyar, Hajiya Mairiga tace "mai girma Gwamna Mai Mala Buni ya cancanci wannan karramawan a wajen shugaban ƙasa Muhammadu Buhari duba ga irin gudumawar da yake bayarwa ta fuskan siyasa, zaman lafiya, hadin kan ƴan ƙasa da kawo ɗaruruwan ayyukan cigaban a Jaharsa ta Yobe da Najeria baki ɗaya". Saboda haka, kungiyar...

Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth ta tallafawa mutanen da iftila'in ruwa tayi musu ta'adi a Gashua.

 Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth ta tallafawa mutanen da iftila'in ruwa tayi musu ta'adi a Gashua.  A jiya lahadi, 9th October, 2022, kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Mairiga ta bada gudumawar kayan abinci da kayan amfani a gida wa mutanen da iftila'in ruwa tayi musu ta'adi a garin Gashua, Karamar hukumar Bade.  Kungiyar, wanda ta mika kayayyakin a hannun shugaban Karamar Hukumar Bade, Hon. Sanda Kara Bade a ofis ɗinsa dake sakaterian karamar hukumar a garin Gashua.  A cikin jawabanta, a lokacin da take mika masa kayan, shugaban kungiyar, Hajiya Mairiga tace "Mu kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network zamuyi duk iya ƙokarin mu domin mu rama alkhairi da alkhairi, ma'ana zamuyi wa Gwamnatin Mai Mala Buni hidima kamar yadda ta inganta rayuwar mata da matasan Jahar Yobe.  Saboda haka, wannan tallafin mun kawo muku ne don mu rage raɗaɗin ɓarnar da ambaliyan tayi wa mutanen Gashua. Kuma, baza muyu ƙa...

Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta ziyarci Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim a Abuja.

 Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta ziyarci Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim a Abuja.  Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim, ƴar majalisan tarayya mai wakiltar mazabar Damaturu, Gujba, Gulani da Tarmuwa a karkashin Jam'iyyar APC ta tarbi kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Mairiga a ofis nata dake National Assembly a birnin Abuja.  A lokacin ziyarar, kungiyar ta mika mata wasikar zama ɗaya daga cikin Patrons nata. Shugaban kungiyar, Hajiya Mairiga ta yabawa Hajiya Khadija akan kekkyawar wakilci da take yiwa mutanen mazabarta tun daga shekarar 2007 har zuwa yanzu. Mairiga ta cigaba da cewa "Kin fitar da mutanen mazabarki kunya a idon duniya, saboda irin ɗaruruwan ayyukan cigaba da kika kawo musu, musamman wajen inganta rayuwar mata da matasa ta fannoni daban-daban" Akan dalilan kafa kungiyar, Hajiya Mairiga ta ce kungiyar, mata da matasa ne suka assasata don su bada gudumawarsu wa gwamnatin Mai Mala Buni da J...