Kungiyar Buni - Gubana Women & Youth Network ta kai ziyara na musamman ofishin Tijjani Musa Tumsa a Abuja.
Kungiyar Buni - Gubana Women & Youth Network ta kai ziyara na musamman ofishin Tijjani Musa Tumsa a Abuja.
......Kungiyar ta naɗa shi a matsayin memba na komitin amintattu.
Kungiyar Buni - Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Gwamnaty Mairiga ta kai ziyara na musamman ofishin jigo cikin ƴan siyasan Najeria kuma gogeggen Dan siyasan Jahar Yobe Alh. Tijjani Musa Tumsa (TMT) a Abuja.
A cikin jawabanta, Hajiya Fatima ta bayyana cewa "Kungiyar, wanda matasa da mata na Jahar Yobe suka assasata don su bada gudumawarsu wa gwamnatin Mai Mala Buni musamman akan kyawawan manufofin cigaban Jahar Yobe da Gwamnatin da ta ɗauko kuma mutane suke moran ta a zahiri"
Mairiga ta ce Insha Allah matasan Jahar Yobe zasu 'rama alkhairi da alkhairi' , saboda ɗaruruwan ayyukan cigaban matasa, bawa matasa muƙaman Gwamnati, inganta rayuwar mata-da-yara musamman wajen kiwon lafiya, bada jari keuta da sauran tsare-tsare masu yawa don inganta rayuwar mata-masu-juna, jarirai da yara ƙanana.
Saboda haka, Mata da matasan Jahar Yobe za suyi kamfen duk biranai da kauyukan Jahar don cigaban Gwamnatin Mai Mala Buni da Jam'iyyar APC baki daya.
Daga karshe, Tijjani Tumsa ya fara da saka wa kungiyar albarka; sannan yayi alwashin zai bada gudumawarsa don nasarar Gwamna Mai Mala Buni, Bola Tinubu da duka ƴan takarkarun Jam'iyyar APC daga sama har ƙasa a zaɓe mai zuwa.
Hajiya Mairiga ta samu rakiyar wasu daga cikin shugabannin kungiyar.
Singed: Mustapha Mohammed Banker,
For Media and Publicity.
Photo by Arfo.
Comments
Post a Comment