Kungiyar Buni-Gubana Women and Youth Network ta naɗa Kwamishinan jinkai da kula da lamuran agaji, Dr. Abubukar Garba Iliya a matsayin memba na komitin amintattu.
Kungiyar Buni-Gubana Women and Youth Network ta naɗa Kwamishinan jinkai da kula da lamuran agaji, Dr. Abubukar Garba Iliya a matsayin memba na komitin amintattu.
A yau litinin, kungiyar BUNI-GUBANA WOMEN & YOUTH NETWORK karkashin jagorancin Hajiya Fatima Gwamnaty Mairiga ta ziyarci ofishin Kwamishinan jinkai da kula da lamuran agaji na Jahar Yobe, Dr. Garba Iliya a inda ta naɗa shi a matsayin memba na komitin amintattu na kungiyar.
Kungiyar, wanda matasa da mata na Jahar Yobe suka hadu suka ƙirkiro da ita don su bada gudumawarsu wa Gwamnatin Mai Mala Buni don ta cigaba da kyawawan manufofin cigaban Jahar Yobe da ta ɗauko kuma mutane suke moran ta a zahiri.
Kama daga; ayyukan cigaban matasa da dama, bawa matasa dama a Gwamnatinsa, inganta rayuwar mata-da-yara musamman wajen kiwon lafiya, bada jari da sauran tsare-tsare masu yawa wa mata masu juna, jarirai da yara ƙanana.
Buni-Gubana Women & Youth Network ta fito da taken ta "rama alkhairi da alkhairi' . Ma'ana, bada zunzurutun gudumawa da hidima tuƙuru ga Gwamnatin Mai Mala Buni da Hon. Idi Barde Gubana don ta cigaba da inganta rayuwar Jahar Yobe.
Hajiya Fatima Gwamnaty Mairiga ta samu rakiyar wasu daga cikin shugabannin kungiyar.
Comments
Post a Comment