Skip to main content

Kungiyar Buni Gubana Women & Youth network ta fara shiriye-shiriyen gudanar da manya-manyan tararruka a Yobe zone-A , zone-B da zone-C.

 Kungiyar Buni Gubana Women & Youth network ta fara shiriye-shiriyen gudanar da manya-manyan tararruka a Yobe zone-A , zone-B da zone-C. 







A yau Talata, kungiyar Buni Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Gwamnaty Mairiga ta fara shiriye-shiriyen gudanar da manya-manyan tararruka na ƙaddamar da shugabanninta na Yobe shi'ar gabas, shi'ar kudu da shi'ar arewa. 


Kamar yadda a baya Kungiyar ta ƙaddamar da shugabanninta na jaha, yanzu haka ta fara shiriye-shiriyen ƙaddamar da na shi'oin uku na jahar, daga nan kuma sai na ƙananan hukumomi 17 da gundumomi 178 na Jahar Yobe baki daya. 


Kungiyar, wanda matasa da mata na Jahar Yobe suka hadu suka ƙirkiro da ita don su bada gudumawarsu wa Gwamnatin Mai Mala Buni don ta cigaba da kyawawan manufofin cigaban Jahar Yobe da ta ɗauko kuma mutane suke moran ta a zahiri. Kama daga; ayyukan cigaban matasa da dama, bawa matasa dama a Gwamnatinsa, inganta rayuwar mata-da-yara musamman wajen kiwon lafiya, bada jari da sauran tsare-tsare masu yawa wa mata masu juna, jarirai da yara ƙanana.

Comments

Popular posts from this blog

Muslim-Muslim ticket: Kungiyar Buni Gubana women and Youth Network ta gana da mabiya addinin kirista a Fika, ta kira su da su marawa Jam'iyyar APC baya.

 Muslim-Muslim ticket: Kungiyar Buni Gubana women and Youth Network ta gana da mabiya addinin kirista a Fika, ta kira su da su marawa Jam'iyyar APC baya.  A jiya Asabar, kungiyar Buni Gubana Women and Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Gwamnaty Mairiga ta ziyarci garin Kamfani dake Karamar hukumar Fika don ganawa da mabiya addinin kirista, tayi musu Kira da su marawa Gwamnatin Mai Mala Buni da Jam'iyyar APC baya ɗari bisa ɗari a zaɓen 2023.  Kungiyar ta jaddada musu cewa kar suyi fargaban zaɓen 'Muslim-Muslim' ticket , wato Dan takaran shugaban ƙasa karkashin Jam'iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu tare da mataimakinsa Senata Kashim Shettima a zaɓen 2023.  Hajiya Mairiga ta ƙara da tunatar dasu wasu ɗaruruwan ayyukan cigaba da Gwamnatin Mai Mala Buni ta kawo wa Jahar Yobe a cikin shekaru uku Kachal na mulkinsa, saboda haka tana bukatansu da marawa Gwamnatinsa baya ɗari bisa ɗari don cigaba ayyukan Alheri.  Haka zalika, tayi musu kira da su za...

Gov. Buni Charge Women and Youth on Patriotism

 Gov. Buni Charge Women and Youth on Patriotism The Buni/Gubana Women and Youth Network, today paid a courtesy call on His Excellency, the Executive Governor of Yobe state, Hon. Mai Mala Buni, at Government House Damaturu. Coordinator of the Network, Hajiya Mairiga Umar, described Governor Buni as the most youth and women friendly governor in Nigeria. She said the essence of creating the network was to appreciate the gesture of the governor to women and youth in the state through dedication and selfless service. Mairiga assured that the Network would work for the success of the Governor Buni administration. Governor Buni urged members of the Network to always have the interest of the state at heart. "You are the leaders of tomorrow, you should develop the spirit of patriotism and selfless to the state and country. Gov. Buni commended the Network for the show of love and concern to his government and state. Signed Mamman Mohammed, DG, Press and Media Affairs.

Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network reshen Karamar hukumar Fika ta ziyarci Mai Martaba Sarkin Fika.

 Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network reshen Karamar hukumar Fika ta ziyarci Mai Martaba Sarkin Fika.  A cikin shiriye-shiriyenta na wayar da kan mutane akan kyawawan manufofi da tsare-tsaren Gwamnatin Mai Mala Buni don su cigaba da marawa Gwamnatinsa da Jam'iyyar APC baya ɗari bisa ɗari, a yau Asabar 24th September, 2022, kungiyar Buni Gubana Women & Youth Network reshen Karamar hukumar Fika ta kai ziyara na musamman wa fadan Mai Martaba Sarkin Fika don neman tabarraki da shawarwari . Shugaban kungiyar, reshen Karamar hukumar Fika, Abubakar Ayuba Idriss tare da sauran membobinsa sun samu rakiyar shugaban kungiyar reshen Yobe zone-B Mohammed Musa Kawuwale shima tare da sauran shuwagannin kungiyar na reshen Yobe zone B. A cikin jawabansu, Abubakar Ayuba Idriss da Mohammed Musa Kawuwale sun bayyanawa Mai martaba cewa kungiyar ta fito ne taken ta na "Rama alkhairi da alkhairi' ma'ana, ƙokarin rama alkhairin da Gwamnatin Mai Mala Buni ta kawo wa Jahar Yobe, m...