Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta naɗa Kwamishinan ma'aikatan ilimin matakin farko da Kwamishinan mata a matsayin masu bawa kungiyar shawara
Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta naɗa Kwamishinan ma'aikatan ilimin matakin farko da Kwamishinan mata a matsayin masu bawa kungiyar shawara.
A Ranar Laraba, kungiyar BUNI-GUBANA WOMEN & YOUTH NETWORK karkashin jagorancin Hajiya Fatima Gwamnaty Mairiga ta ziyarci ofishin Kwamishinan ma'aikatan ilimin matakin farko Dr. Muhammad Sani Idriss da Kwamishinan ma'aikatan mata Hajiya Hauwa Abubakar a matsayin masu bawa kungiyar shawara.
Kwamishinonin sun yaba da ƙokarin matasa da matan da suka ƙirkiro Kungiyar don ƙokarin "rama alkhairi da alkhairi' . Ma'ana, bada zunzurutun gudumawa da hidima tuƙuru ga Gwamnatin Mai Mala Buni da Hon. Idi Barde Gubana don ta cigaba da inganta rayuwar Jahar Yobe.
Hajiya Mairiga ta samu rakiyar wasu daga cikin shugabannin kungiyar.
Comments
Post a Comment