Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network tana taya Gwamna Mai Mala Buni murnan samun karramawa na 'CON' daga shugaban ƙasa Buhari.
Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network tana taya Gwamna Mai Mala Buni murnan samun karramawa na 'CON' daga shugaban ƙasa Buhari.
Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Mairiga tana taya mai girma Gwamna Mai Mala Buni murnan samun karramawa na 'CON' daga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a wajen taron karrama ƴan ƙasa da a ake gudanar da ita a babban dakin taro na International Conference Centre, Abuja.
Bikin an shiriya tana don karrama ƴan Nigeria da suke yin ƙokari wajen bada gudumawarsu don tabbatar da zaman lafiya, hadin kan ƴan ƙasa, yiwa ƙasa hidima da cigaban Najeria baki ɗaya.
Shugaban kungiyar, Hajiya Mairiga tace "mai girma Gwamna Mai Mala Buni ya cancanci wannan karramawan a wajen shugaban ƙasa Muhammadu Buhari duba ga irin gudumawar da yake bayarwa ta fuskan siyasa, zaman lafiya, hadin kan ƴan ƙasa da kawo ɗaruruwan ayyukan cigaban a Jaharsa ta Yobe da Najeria baki ɗaya". Saboda haka, kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network, amadadin mata da matasan Jahar Yobe tana taya sa farin ciki, murna, tare da yi masa addu'ar Allahu ya taimake shi, ya bashi kariya, ya rufa masa asiri kuma ya sanya albarka a wannan lambar yabon don alfarmar ANNABI MUHAMMAD RASULALLAHI SALLALAHU ALAIHI WASSALAM SALLALAHU ALAIHI WASSALAM SALLALAHU ALAIHI WASSALAM
Comments
Post a Comment