Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta ziyarci Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim a Abuja.
Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim, ƴar majalisan tarayya mai wakiltar mazabar Damaturu, Gujba, Gulani da Tarmuwa a karkashin Jam'iyyar APC ta tarbi kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Mairiga a ofis nata dake National Assembly a birnin Abuja.
A lokacin ziyarar, kungiyar ta mika mata wasikar zama ɗaya daga cikin Patrons nata. Shugaban kungiyar, Hajiya Mairiga ta yabawa Hajiya Khadija akan kekkyawar wakilci da take yiwa mutanen mazabarta tun daga shekarar 2007 har zuwa yanzu. Mairiga ta cigaba da cewa "Kin fitar da mutanen mazabarki kunya a idon duniya, saboda irin ɗaruruwan ayyukan cigaba da kika kawo musu, musamman wajen inganta rayuwar mata da matasa ta fannoni daban-daban"
Akan dalilan kafa kungiyar, Hajiya Mairiga ta ce kungiyar, mata da matasa ne suka assasata don su bada gudumawarsu wa gwamnatin Mai Mala Buni da Jam'iyyar APC baki daya. "Haka zalika, kungiyar ba zatayi ƙasa-a-guiwa ba sai ta tabbatar da duk ƴan takarkarun Jam'iyyar APC tun daga matakin shugaban ƙasa har zuwa ƴan majalisun jaha sunyi nasara a zaɓe mai zuwa don alfarmar Annabi Muhammadu Rasulullahi (S.A.W)".
Ita kuma acikin jawabanta, Hajiya Khadija tace "na kawo ku cikin ofis ɗina ne don kuzo kuga irin aikin da kuka turo mu muyi muku wannan wuri; shi yasa tun jiya na sanar da duk Jami'an tsaro da ma'aikatan wannan wuri cewa zanyi baƙi daga jaha ta"
Daga karshe, ta karrama ƴan kungiyar tare da yin alwashin bada gudumawarsa don nasarar Gwamna Mai Mala Buni, Bola Tinubu da duka ƴan takarkarun Jam'iyyar APC daga sama har ƙasa a zaɓe mai zuwa.
Hajiya Mairiga ta samu rakiyar wasu daga cikin shugabannin kungiyar.
Mustapha Gujba Banker.
Photo by Arfo.
Comments
Post a Comment