Ƙungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta ziyarci shugaban majalisan Dattawan Nigeria (Senate President) Da mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa a Abuja..
Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta ziyarci shugaban majalisan Dattawan Nigeria (Senate President) Da mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa a Abuja..
Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Gwamnaty Mairiga ta kai ziyara na musamman ofis ɗin shugaban majalisan dattawan Najeria, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan GCON, da mataimakin shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa (Na Arewacin Najeria), Sanata Abubakar Kyari a Abuja.
Ziyarar, wanda shugaban kungiyar ta jagoranta an fara ta ne da taya shugaban majalisan dattawan murman samun lambar yabo na 'GCON' daga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Haka zalika, kungiyar ta ziyarci Sanata Abubakar Kyari ne don tattaunawa da shi akan lamuran Jam'iyyar APC (a mataki na ƙasa) musamman abubuwan da suka shafi Jam'iyyar da zaɓen 2023.
Daga ƙarshe, Ƙungiyar ta yiwa Sanata Ahmed Ibrahim Lawan addu'ar Allahu ya taimake shi, ya dafa masa, sannan ya albarkaci sabuwar lambar yabon da ya samu.
Comments
Post a Comment