Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth ta tallafawa mutanen da iftila'in ruwa tayi musu ta'adi a Gashua.
Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth ta tallafawa mutanen da iftila'in ruwa tayi musu ta'adi a Gashua.
A jiya lahadi, 9th October, 2022, kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Mairiga ta bada gudumawar kayan abinci da kayan amfani a gida wa mutanen da iftila'in ruwa tayi musu ta'adi a garin Gashua, Karamar hukumar Bade.
Kungiyar, wanda ta mika kayayyakin a hannun shugaban Karamar Hukumar Bade, Hon. Sanda Kara Bade a ofis ɗinsa dake sakaterian karamar hukumar a garin Gashua.
A cikin jawabanta, a lokacin da take mika masa kayan, shugaban kungiyar, Hajiya Mairiga tace "Mu kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network zamuyi duk iya ƙokarin mu domin mu rama alkhairi da alkhairi, ma'ana zamuyi wa Gwamnatin Mai Mala Buni hidima kamar yadda ta inganta rayuwar mata da matasan Jahar Yobe.
Saboda haka, wannan tallafin mun kawo muku ne don mu rage raɗaɗin ɓarnar da ambaliyan tayi wa mutanen Gashua. Kuma, baza muyu ƙasa a guiwa ba wajen cigaba da irin wannan hidima a Jahar Yobe".
Shi kuma a cikin jawabansa, Alhaji Sanda Kara Bade ya fara da jinjinawa kungiyar a kan namijin ƙokari da tayi, "wanda a tarihin Jahar Yobe, ba'a cika samun kungiyoyin siyasa suna bada irin wannan gudumawar ba. Saboda, lalle kungiyar ku na Buni-Gubana Women & Youth Network tazo da kekkyawar niyya wajen tallafawa Gwamnatin Mai Mala Buni".
Daga karshe, ya saka wa kungiyar albarka, yayi mata addu'a tare da fatan Alheri.
Cikin kayayyakin da kungiyar ta kai sun hada da buhuhunan garin masara guda 50, kwalayen sabulun wanki, kwalayen makaroni, kwalayen maggi, kwalayen Omo, manya-manyan jarakun mai-na-miya, bokati guda 30 da buta guda 30.
Comments
Post a Comment