Ambaliyan ruwa: Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta kai tallafi garin Koromari, yankin Dapchi.
Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Gwamnaty Mairiga ta bada gudumawar kayan abinci da kayan amfani-a-gida wa mutanen da iftila'in ruwa yayi musu ta'adi a garin Koromari dake yankin Dapchi, karamar hukumar Bursari.
Tawagar kungiyar, wanda sukayi tafiya na wasu lokuta akan kwale-kwale a cikin ruwa don ƙokarin kai agaji wa bayin Allah wanda iftila'in ambaliyan ya shafe su.
A lokacin ziyarar, Hajiya Mairiga tace "mu kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network munzo ne domin mu jajanta muku akan asarar dukiyoyin ku da kukayi sanadiyar ambaliyan. Shi yasa muka zo muku da wannan tallafin dai-dai karfin mu domin ta rage muku raɗaɗin ɓarnar da ambaliyan yayi muku".
Shi kuma a cikin jawabansa, Mai garin, a madadin mutanen garinsa, Koromari, ya fara da jinjinawa kungiyar a kan namijin ƙokari da tayi, "wanda a tarihi, ban taɓa ganin irin wannan Kungiyar ba, wanda ta taso da kyawawan manufofi da kekkyawar niyya domin bada gudumawa a cigaban Jahar Yobe baki ɗaya. Saboda haka, Mungode mungode mungode"
Daga karshe, kungiyar tayi musu addu'ar Allahu ya mayar musu duk abun da suka rasa da alkhairi.
Sannan, ta damka kayan a hannun mai gari tare da tawagarsa.
Cikin kayayyakin da kungiyar ta kai sun hada da;
(a) Buhuhunan garin masara guda 50, kwalayen sabulun wanki,
(b) kwalayen taliya supergetti,
(c) kwalayen maggi,
(d) kwalayen klin Omo,
(e) manya-manyan jarakun man-miya,
(f) bokati guda 20
(g) buta guda 30.
Comments
Post a Comment