Kungiyar Buni Gubana Women & Youth network ta fara shiriye-shiriyen gudanar da manya-manyan tararruka a Yobe zone-A , zone-B da zone-C.
Kungiyar Buni Gubana Women & Youth network ta fara shiriye-shiriyen gudanar da manya-manyan tararruka a Yobe zone-A , zone-B da zone-C. A yau Talata, kungiyar Buni Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Gwamnaty Mairiga ta fara shiriye-shiriyen gudanar da manya-manyan tararruka na ƙaddamar da shugabanninta na Yobe shi'ar gabas, shi'ar kudu da shi'ar arewa. Kamar yadda a baya Kungiyar ta ƙaddamar da shugabanninta na jaha, yanzu haka ta fara shiriye-shiriyen ƙaddamar da na shi'oin uku na jahar, daga nan kuma sai na ƙananan hukumomi 17 da gundumomi 178 na Jahar Yobe baki daya. Kungiyar, wanda matasa da mata na Jahar Yobe suka hadu suka ƙirkiro da ita don su bada gudumawarsu wa Gwamnatin Mai Mala Buni don ta cigaba da kyawawan manufofin cigaban Jahar Yobe da ta ɗauko kuma mutane suke moran ta a zahiri. Kama daga; ayyukan cigaban matasa da dama, bawa matasa dama a Gwamnatinsa, inganta rayuwar mata-da-yara musamman wajen kiwon lafiya,...