Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network reshen Karamar hukumar Fika ta ziyarci Mai Martaba Sarkin Fika.
Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network reshen Karamar hukumar Fika ta ziyarci Mai Martaba Sarkin Fika.
A cikin shiriye-shiriyenta na wayar da kan mutane akan kyawawan manufofi da tsare-tsaren Gwamnatin Mai Mala Buni don su cigaba da marawa Gwamnatinsa da Jam'iyyar APC baya ɗari bisa ɗari, a yau Asabar 24th September, 2022, kungiyar Buni Gubana Women & Youth Network reshen Karamar hukumar Fika ta kai ziyara na musamman wa fadan Mai Martaba Sarkin Fika don neman tabarraki da shawarwari .
Shugaban kungiyar, reshen Karamar hukumar Fika, Abubakar Ayuba Idriss tare da sauran membobinsa sun samu rakiyar shugaban kungiyar reshen Yobe zone-B Mohammed Musa Kawuwale shima tare da sauran shuwagannin kungiyar na reshen Yobe zone B.
A cikin jawabansu, Abubakar Ayuba Idriss da Mohammed Musa Kawuwale sun bayyanawa Mai martaba cewa kungiyar ta fito ne taken ta na "Rama alkhairi da alkhairi' ma'ana, ƙokarin rama alkhairin da Gwamnatin Mai Mala Buni ta kawo wa Jahar Yobe, musamman ta bangaren cigaban mata da matasa ta fannin Ilimi, aikin-yi, kiwon lafiya, da sauransu.
Daga karshe, Mai martaba, Alh. Muhammad Ibn Abali Muhammad Idrissa ya jinjinawa kungiyar, kuma gargadi shuwagannin kungiyar da su haɗa kawunansu, kuma su guji duk abinda zai iya kawo rashin jituwa a tsakaninsu.
Ya rufe da yiwa kungiyar addu'a tare da saka mata Albarka.
Comments
Post a Comment