Muslim-Muslim ticket: Kungiyar Buni Gubana women and Youth Network ta gana da mabiya addinin kirista a Fika, ta kira su da su marawa Jam'iyyar APC baya.
Muslim-Muslim ticket: Kungiyar Buni Gubana women and Youth Network ta gana da mabiya addinin kirista a Fika, ta kira su da su marawa Jam'iyyar APC baya.
A jiya Asabar, kungiyar Buni Gubana Women and Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Gwamnaty Mairiga ta ziyarci garin Kamfani dake Karamar hukumar Fika don ganawa da mabiya addinin kirista, tayi musu Kira da su marawa Gwamnatin Mai Mala Buni da Jam'iyyar APC baya ɗari bisa ɗari a zaɓen 2023.
Kungiyar ta jaddada musu cewa kar suyi fargaban zaɓen 'Muslim-Muslim' ticket , wato Dan takaran shugaban ƙasa karkashin Jam'iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu tare da mataimakinsa Senata Kashim Shettima a zaɓen 2023.
Hajiya Mairiga ta ƙara da tunatar dasu wasu ɗaruruwan ayyukan cigaba da Gwamnatin Mai Mala Buni ta kawo wa Jahar Yobe a cikin shekaru uku Kachal na mulkinsa, saboda haka tana bukatansu da marawa Gwamnatinsa baya ɗari bisa ɗari don cigaba ayyukan Alheri.
Haka zalika, tayi musu kira da su zaɓi duk ƴan takarkaru karkashin Jam'iyyar APC Sak daga sama har ƙasa a zaɓen 2023.
Hajiya Mairiga ta samu rakiyar shugaban mata na Jam'iyyar APC na Jahar Yobe Hajiya Ladi Jibrin, shugaban kungiyar na reshen Yobe ta gabas Alh. Abdullahi Gulani (Okocha), mai bawa Gwamna shawara na musamman akan lamuran addini Emmanuel Degubi da wasu jiga-jigan kungiyar.
Comments
Post a Comment