Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta naɗa Hon. Abdullahi Usman Kukuwa a matsayin mai bawa kungiyar shawara.
Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta naɗa Hon. Abdullahi Usman Kukuwa a matsayin mai bawa kungiyar shawara.
BUNI-GUBANA WOMEN & YOUTH NETWORK karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Gwamnaty Mairiga ta ziyarci Kwamishinan sufuri da makamashi na Jahar Yobe, Hon. Abdullahi Usman Kukuwa, a inda ta naɗa shi mai bawa kungiyar shawara (Adviser).
A lokacin ziyaran, Hajiya Mairiga da Hon. Abdu Okocha sun yaba masa akan ƙokari da nasarori da Gwamnatin Mai Mala Buni ta samu musamman a ma'aikatarsa; misali , babban tashan jiragen sama mai jidon kaya wanda aka kammala kwanannan da ɗaruruwan ayyukan wutan lantarki wanda aka aiwatar dasu a ɗaruruwan kauyuka da biranai na Jahar Yobe karkashin ƙokari da kulawarsa.
Haka zalika, a cikin jawabanta, Hajiya Mairiga ta bayyana cewa an kafa kungiyar ne don 'rama alkhairi da alkhairi', matasa da mata sun fito ne domin su bada gudumawarsu wa Gwamnatin Mai Mala Buni don ta cigaba da kyawawan manufofin cigaban Jahar Yobe da ta ɗauko kuma mutane suka moran ta a zahiri. Daga ayyukan cigaban matasa da dama, bawa matasa dama a Gwamnatinsa, inganta rayuwar mata-da-yara musamman wajen kiwon lafiya, bada jari da sauran tsare-tsare masu yawa wa mata masu juna, jarirai da yara ƙanana.
Hajiya Mairiga ta samu rakiyar wasu daga cikin shugabannin kungiyar.
Comments
Post a Comment