Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta naɗa GREEN AND BLUE a matsayin mai bawa kungiyar shawara.
Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta naɗa GREEN AND BLUE a matsayin mai bawa kungiyar shawara.
kungiyar Buni Gubana Women and Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Gwamnaty Mairiga ta ziyarci ofishin Alh. Mallam Kura wanda aka fi sani da GREEN AND BLUE, ta naɗa shi mai bawa kungiyar shawara (Adviser).
A cikin jawabanta, Hajiya Mairiga ta bayyana cewa kungiyar BUNI GUBANA WOMEN AND YOUTH NETWORK ta fito ne da taken ta na 'rama alkhairi da alkhairi', ma'ana, matasa da matan kungiyar sun fito ne domin su bada gudumawarsu wa Gwamnatin Mai Mala Buni musamman wajen aiwatar da ayyukan cigaba da takeyi don inganta rayuwar mutanen Jahar Yobe.
Hajiya Mairiga, ta ƙara da jinjinawa Green And Blue akan ƙokari da yakeyi wajen keutatawa da tallafawa mutane don cigaban Gwamnatin Mai Mala Buni.
Hajiya Mairiga ta samu rakiyar wasu daga cikin shugabannin kungiyar. Buni-Gubana Women and Youth Network. #BUNI_GUBANA_WOMEN_AND_YOUTH_NETWORK
Comments
Post a Comment