Kungiyar Buni - Gubana Women & Youth Network ta ziyarci Ministan wutan lantarkin Najeria, Engr. Abukakar D. Aliyu a Abuja
Kungiyar Buni - Gubana Women & Youth Network ta ziyarci Ministan wutan lantarkin Najeria, Engr. Abukakar D. Aliyu a Abuja.
......Kungiyar ta bashi wasikar zama ɗaya daga cikin Patrons nata, da lambar yabo a bisa ayyukan cigaba da ya kawo wa Jahar Yobe.
Kungiyar Buni - Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Umar Mairiga ta kai ziyara na musamman ofishin babban Ministan wutan lantarkin Najeria, Engr. Abubakar D. Aliyu (Jarman Potiskum) dake Power House a birnin Abuja.
A lokacin ziyarar, shugaban kungiyar ta fara da yaba wa Ministan a bisa ƙokari da yakeyi wajen ganin Jahar Yobe ta mori Gwamnatin tarayya da ayyukan cigaba, musamman ayyukan da suke karkashin ofishinsa.
Hajiya Mairiga ta jaddadawa Ministan cewa kungiyar ta shiriya tsaf domin rama "alkhairi da alkhairi" , ma'ana, kasancewar Gwamnatin Mai Mala Buni ta inganta rayuwar mutanen Jahar Yobe baki ɗaya musamman ta ɓangaren cigaban matasa, mata da yara ƙanana ta fannin kiwon lafiya, Ilimi, raba maƙaman Gwamnati, da sauransu. Saboda haka, kungiyar ta fito da shirin shiga duk lunguna da saƙo na Jahar Yobe don jawo hankulan mutanen biranai na kauyuka don su mara wa Gwamnatin Mai Mala Buni da Jam'iyyar APC baya ɗari bisa ɗari. Haka zalika, kungiyar zata bi duk dabaru da salon kanfen don ganin duk ƴan takarkarun Jam'iyyar APC tun daga shugaban ƙasa har zuwa ƴan majalisun jaha sunyi nasara a zaɓe mai zuwa.
Shi kuma a cikin jawabansa, Jarman Potiskum ya yaba wa mata da matasan da suka hadu - suka ƙirkiro Kungiyar don nasarar Gwamnatin Mai Mala Buni da Jam'iyyar APC baƙi daya. Ya cigaba da cewa yana bibiyan kungiyar tun daga kafuwarta har zuwa yanzu a kafofin sada zumunta, hankalinsa ta karkata kan kungiyar sosai don irin kyawawan manufofi da tsare-tsare cikin Ilimi da basira da kungiyar ta fito dashi.
Daga karshe, kungiyar ya mika masa wasikar zama Patron nata tare da lambar yabo a bisa ayyukan cigaba da ya kawo wa Jahar Yobe.
Singed
Mustapha Mohammed Gujba.
The Political Banker.
for Media & Publicity.
#BUNI_GUBANA_WOMEN_AND_YOUTH_NETWORK
Comments
Post a Comment