Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta naɗa Dan Madamin Fika a matsayin mai bawa kungiyar shawara.
Kungiyar Buni-Gubana Women & Youth Network ta naɗa Dan Madamin Fika a matsayin mai bawa kungiyar shawara.
Aranar litinin, kungiyar BUNI-GUBANA WOMEN & YOUTH NETWORK karkashin jagorancin Hajiya Fatima Gwamnaty Mairiga ta ziyarci Alh. Umaru Abdulmalik (Dan Madamin Fika) a garin Potiskum, a inda ta naɗa shi mai bawa kungiyar shawara (Adviser).
Kungiyar, wanda matasa da mata na Jahar Yobe suka hadu suka ƙirkiro da ita don su bada gudumawarsu wa Gwamnatin Mai Mala Buni don ta cigaba da kyawawan manufofin cigaban Jahar Yobe da ta ɗauko kuma mutane suke moran ta a zahiri. Kama daga; ayyukan cigaban matasa da dama, bawa matasa dama a Gwamnatinsa, inganta rayuwar mata-da-yara musamman wajen kiwon lafiya, bada jari da sauran tsare-tsare masu yawa wa mata masu juna, jarirai da yara ƙanana.
Hajiya Mairiga ta samu rakiyar wasu daga cikin shugabannin kungiyar.
Comments
Post a Comment