Kungiyar Buni Gubana Women & Youth Network ta gudanar da babban taro a garin Potiskum.
Aranar Asabar, 17th September, 2022, kungiyar Buni Gubana Women & Youth Network karkashin jagorancin Hajiya Fatima Gwamnaty Mairiga ta gudanar da babban taron kaddamar da kungiyar, shi'ar Yobe ta kudu a garin Potiskum.
Taron wanda aka gudanar da ita a cikin ɗakin taro na FCE Potiskum ta samu halartan manya-manyan Jami'an Gwamnati, ƴan kasuwa, ƴan siyasa da sauran ɗaruruwan maza da mata wanda suka zo daga sassan Jahar Yobe don halartan taron.
A wajen taron, an mika wa shugabannin kungiyar na yankin Yobe ta kudu, tare da shugabanninta na kananan hukumomi guda hudu na yankin (Potiskum, Fika, Nangere da Fune) wasikar fara aiki a matsayinsu na shugabannin kungiyar.
Cikin manya-manyan baƙi da suka halarci taron akwai wakilin shugaban Jam'iyyar APC na Jahar Yobe Alh. Usman Arjali, mataimakin shugaban Karamar hukumar Potiskum, shugaban mata na Jam'iyyar APC na Jahar Yobe Hajiya Ladi Jibrin, Dr. Dauda Atiyaye, Dr. Kagu Abubakar, shugaban Jam'iyyar APC na Potiskum Alh. Bala Musa Lawan, Sarkin Ado, da sauransu.
A cikin jawabanta, shugaban kungiyar na jaha, Hajiya Fatima Umar Mairiga, ta jaddada cewa kungiyar ta fito ne don "rama alkhairi da alkhairi" ma'ana, bada gudumawa don ganin Gwamnatin Mai Mala Buni ta cigaba da aiwatar da ayyukan Alheri a duk sassan Jahar Yobe. Haka zalika, duk ƴan takarkaru karkashin Jam'iyyar APC tun daga shugaban ƙasa har zuwa Dan majalisa sunyi nasara a zaɓen 2023.
Comments
Post a Comment